Atiku ya gana da jagororin addini a jihar Filato

Da safiyar yau ne dantakarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya gana da Sarkin Wase Muhammadu Haruna, shugaban kungiyar Jama’atul Nasarul Islam reshen jihar Filato.

Har ila yau Atiku ya gana da shugaban mabiya darikar cocin Anglican a jihar, Archbishop Benjamin Yashi.

Atiku cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ya yi ganawar a kokarin cigaba da lalubo hanyoyin sake hada kan Najeriya.

More from this stream

Recomended