Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a Lafia na jihar Nasarawa.
Da taron da aka gudanar ya mayar da hankali kan batun tsaro da kuma bangaren hakar ma’adanai.
A yayin taron Tinubu ya ci alwashin bijiro da tsare-tsare da za su bunkasa bangarorin biyu.