Rundunar sojan saman Najeriya ta samu nasarar kai farmaki kan fadar rikakken dan bindiga Halilu dake Zamfara.
Yan bindiga da basu gaza 30 ba ne aka kashe a yayin farmakin kamar yadda wata majiyar tsaro ta fadawa jaridar PR Nigeria.
Halilu ya kasance sanannen mai safarar makamai ga yan bindigar da suke jihohin Katsina da Zamfara
Mazauna yankin dai na ganin Halilu a matsayin daya daga cikin yan bindigar da suka fi kowa kudi a yankin.
Wasu bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu sun bayyana cewa Halilu ya shirya ganawa da yaransa da sassafe a maboyarsa dake Maradun a jihar Zamfara.