Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta ce jazaman ne jam’iyyun siyasar ƙasar su yi aiki sau da ƙafa da tsarin dimokraɗiyya a cikin gida, wajen gudanar da zaɓukansu na fid da gwani gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
Ta ce matuƙar wata jam’iyya ta gaza aiki da tanade-tanaden dokar zaɓen 2022 a zaɓenta na fid da gwani, ba za ta karɓi ɗan takarar da jam’iyyar ta gabatar mata ba.
A sanarwar da Hukumar zaɓe ta INEC ta fitar ranar Talata, ta ce dole ne sai ‘yan takarar da jam’iyyu za su fitar daga mazaɓu guda 1,491 da za su shiga zaɓen 2023, su fito ta hanyar dimokraɗiyya da zaɓen fid da gwani mai sahihanci da gaskiya bisa tanadin sashe na 29 da na 84 na dokar zaɓen 2022.
A cewarta zaɓen fitar da gwani na jam’iyyun, sai ya dace da tanade-tanaden tsarin mulkin jam’iyyun da tsare-tsaren dokar zaɓe da kuma sauran ƙa’idojin INEC.
Sanarwar ta ce kamar yadda doka ta tanada, hukumar zaɓe za ta sa ido kan zaɓen fitar da gwanin kowacce jam’iyya da ta sanar da hukumar a shari’ance bisa tanadin sashe na 82 ƙaramin sashe na ɗaya da ƙaramin sashe na 5 na dokar zaɓe.
Ta ce duk wata jam’iyya da ta gaza sanar da hukumar game da duk wani babban taro da za ta gudanar da nufin fitar da ‘yan takarar da za su tsaya wani zaɓe kamar yadda dokar zaɓe ta yi tanadi, hakan ya rusa sahihancin babban taron.
INEC ta ce jazaman ne sai an gudanar da zaɓukan fitar da gwani a mazaɓu daban-daban kamar yadda sashe na 84 na dokar zaɓe ya ce don kuwa in ji INEC saɓa doka ne a gudanar da zaɓen fitar da gwani a wajen wata mazaɓa don fitar da wani da takara.
Don haka hukumar zaɓe ba za ta sa ido kan irin wannan zaɓen fitar da gwanin ba kuma ba za ta karɓi sakamakonsa ba.
Sanarwar ta INEC ta yi kira ga jam’iyyun siyasa su guji gwara kan ‘ya takara yayin zaɓukan fid da gwani, wanda ka iya haddasa shari’o’in babu gaira babu dalili da za su iya janyo gaza fitar da ‘yan takarar da za su shiga zaɓe a wasu mazaɓu.
INEC ta ce zaɓen fitar da gwani shi ne na uku cikin al’amura 14 na jadawalin zaɓen 2023.
A cewar sanarwar INEC, jam’iyyu na da kwana 61 su kammala zaɓen fitar da gwani na masu neman takarar shugaban ƙasa da gwamononi da kuma ‘yan majalisun tarayya.

