
Ta yi nasara ne da abincin da ta girka da ta laka wa suna L’abbraccio – wato runguma.
Eboigbodin , wacce ta zo Italiya tare da danginta bayan ta gama kuruciyarta a Najeriya ta ce, “Rungumar babbar alama ce ta hadin kai tsakanin abubuwa biyu daban-daban, na nesa, wani sa’in kuma na kusa.”
“A lokacin da nake MasterChef na koyi bude zuciyata ga abin da ban sani ba kuma da abubbuwan da na tashi da shi ba tare da tsoro ko son zuciya ba , kuma na sanya shi cikin abinci na ta hanya mai kyau.
“Ina so in bayyana ma’anar hakan a gare ni a cikin darussa hudu na wannan girkin”.
Eboigbodin ta lashe tukuicin Yuro 100,000 da zinarin gani na gwanaye, da kuma ikon buga littafin girke-girkenta. (ANSA).

