Abin da ya sa na ce jin waƙa ba haramun ba ne – Sheikh Ibrahim Khalil

Abin da ya sa na ce jin waƙa ba haramun ba ne – Sheikh Ibrahim Khalil

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan a Najeriys Sheikh Ibrahim Khalil, ya kare wata fatawa da ya bayar a baya-bayan nan da ke halatta jin waƙa, saɓanin fatawar da malamai da dama takwarorinsa suka sha bayarwa da ke haramta sauraron waƙar.

Kwanan baya ne fatawar malamin ta haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta yada bidiyonsa, wasu na karɓar fatawar, wasu kuwa na ganinta a matsayin wani yunƙuri na shagaltar da jama’a.

Sai dai yayin wata hira da BBC Hausa, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce yana nan a kan bakarsa.

‘Inda za ka san waƙa tsari ne na Allah kuma ɗabi’a ce ta dan adam shine idan ka ɗauki yaro dan shekara ɗaya ko biyu da ka sa masa waƙa za ka ga yana nuna alamar zai yi rawa, yana nuna jin daɗinsa, sannan idan ka dubu duk wani dattijo za ka ga ya haddace wata waƙa irin ta da” inji Malamin.

Ya ƙara da cewa ”Ko da Annabi Muhammad ya saurari wakoki, waɗanda suke masu kyau, har ma watarana ya taɓa cewa wani ya yi masa wakar wane, ya ambaci wanda ba musulmi bane ba ma, sai da ya rera masa baiti ɗari a waƙar wannan mutumi” inji shi.

More from this stream

Recomended