Robert Lewandowski ya ci kwallo na 43 a Bayern Munich a shekarar 2021, ya kuma haura tarihin Gerd Muller a cin kwallaye a Bundesliga a shekara daya.
Dan wasan tawagar Poland, mai shekara 33, shine ya ci na hudu saura minti uku a tashi a karawar da Bayern Munich ta casa Wolfsburg 4-0 a Allianz Arena a gasar Bundesliga.
Gerd Muller ya kafa tarihin cin kwallo 42 a gasar Bundesliga a shekarar 1972, tun daga lokacin ba wanda ya ci yawan kwallayen a shekara daya sai a wannan lokacin.
Nasarar da Bayern ta yi ya sa ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki tara tsakaninta da Borussia Dortmund.
A watan Mayu, Lewandowski ya haura tarihin tsohon dan kwallon Bayern Munich, Muller mai shekara 49 da cin kwallo 41 a kakar 2020-21.
Thomas Muller, wanda ya buga wasa na 400 a babbar gasar Jamus ne ya fara cin kwallo a minti na bakwai da taka leda daga baya Dayot Upamecano ya kara na biyu.
Leroy Sane ne ya kara na uku, sannan Lewandowski ya ci na hudu.