Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan wani bincike na musamman da BBC Hausa ta yi kan aikin samar da wutar lantarki a Mambila da ke jihar Taraba.
BBC ta yi tattaki zuwa wurin da aka ware don gina tashar wutar lantarkin Mambila, amma kuma hoton bidiyon da ta dauko daga can ya nuna cewa kwata-kwata ba a fara aikin ba, shekaru 40 bayan fara magana kansa.
A martanin da ya yi lokacin hira da BBC, babban mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan yada labarai Malan Garba Shehu ya ce ”kudin da aka ayyana aikin zai lakume da suka kai sama da dala biliyan hudu bashi ne da zai fito daga bankin China Exim Bank”.
Sai dai a cewarsa takaddama tsakanin gwamnati da wani dan kwangila ya hana bankin ba da bashi.
“Akwai wani dan kasuwa a Najeriya da a ke kira Leno Adesanya, wanda ke ikirarin cewa gwamnatin da ta wuce ta ba shi aikin kawo ‘yan kwangilar da za su yi aikin tashar Mambila.”
Kuma a cewar Malam Garba Shehu binciken da ma’aikatar shari’a a gwamnatinsu ta yi ya nuna cewa “babu inda aka kai kwangilar ofishin tantance kwangiloli don neman amincewa.”
“A kan haka dan kwangilar ya kai gwamnatin Najeriya kara a kwamitin daidaito na ‘yan kasuwa a Paris da cewa yana neman diyyar dala miliyan 200 daga Najeriya kafin ya saki wannan kwangila wanda hakan ya sa China ta dakatar da ba da bashin,” in ji Garba Shehu.
Kakakin ya kara da cewa da zarar kudi ya samu babu bata lokaci ba gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta fara aiki samar da tashar wutar ta Mambila.
“To amma aikin zai yiwu ne idan dan kwangilar da ke ikirarin neman diyya ya nuna kishi ya janye karar da ya kai gwamnati”.
An bai wa gwamnatin jihar Taraba $1m don kayyade girman tabkin
Tun bayan fitar da rahoton na BBC yan Najeriya da kuma masu ruwa da tsaki ke martani a kai.
A martanin dan majalisa mai wakiltar Taraba Ta Tsakiya Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya ce aikin tashar wutar Mambila ba karamin aiki ba ne.
Ya ce a saninsa “an bai wa gwamnatin jihar Taraba naira biliyan daya na safiyo don kayyade girman tabkin amma har yanzu ba ta gama aikinta ba.”
To amma a cewarsa a ganinsu bai kamata ba a ce gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnatin jiha irin wadannan kudade da sunan safiyo ba.
An dade ana ta maganganu daban-daban da zargin jan kafa wurin aikin tashar Mambila, da kuma son sanin inda aka kwana wajen aiwatar da aikin da ake sa ran zai samar wa Najeriya isasshiyar wutar lantarki.
Ko da a shekarar 2020 ma a wata hira da BBC, tsohon ministan wutar lantarki Injiya Saleh Mamman ya ce akwai tatsuniya kan batun wutar ta Mambila.
Idan har aikin ya kammala tashar za ta kasance mafi girma a Najeriya kuma daya daga cikin manyan tashoshin wuta a nahiyar Afirka.
Najeriya na samar da megawat na wuta tsakanin 5,000 zuwa 5400 a lokaci da dukkan tashoshin samar da wuta na kasar ke cikakken aiki.