Me ya sa ‘yan bindiga suka koma satar sarakuna a Najeriya?

Sarakuna a Jihar Kaduna

Asalin hoton, KDSG/KAJURU EMIRATE

Bayanan hoto,
Sarkin Jaba Danladi Gyet Maude (hagu) da Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu waɗanda ‘yan fashin daji suka sace

Satar mutane domin neman kuɗin fansa abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya kuma bai tsaya a kan daidaikun mutane da ɗalibai ba, hatta sarakunan gargajiya ba su tsira ba.

A cikin mako biyu sarakuna uku aka yi garkuwa da su, kodayake an saki biyu daga cikinsu amma na baya-bayanan har yanzu na hannun ‘ƴan bindigar.

Sarakunan da suka shiga wannan hali sun haɗa da Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu, wanda aka yi garkuwa da shi tare da iyalan gidansa har da jariri. Duk da cewa daga bisani an sako shi sauran iyalan na hannun masu gatrkuwa da suka nemi kudin fansa har naira miliyan 200.

Kalizaka, a Jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya an yi garkuwa da wani basarake amma daga bisani aka sako shi ba tare da wani karin bayani kan ko an biya kudin fansa ba ko akasin haka.

Na baya-bayanan shi ne sarkin Jaba da ke Kaduna, Mr Danladi Gyet Maude, wanda aka sace da yammacin ranar Litinin a jihar Nasarawa yana hanyar tafiya gonarsa.

Ƴan sanda sun ce suna iya bakin kokarinsu domin gano inda yake, sai dai bayanan da aka tattara sun nuna cewa ‘ƴan bindiga a kan babura ne suka yi awon gaba da shi.

Basaraken mai shekara sama da 80 ya kasance mutum na uku cikin sarakunan da aka kai wa hari cikin mako biyu a Najeriya.

‘Neman kuɗin fansa mai gwaɓi’

A matsayinsu na ma’adanan al’adun al’umma, ana matukar girmama sarakuna a cikin al’umma. Kuma har yanzu babu wani sahihin bayanai kan abin da ya sa ‘ƴan bindiga suka koma kai musu farmaki.

Sai dai masu sharhi irinsu Dokta Muhammad Kabir Isa na cewa ‘ƴan bindiga a galibin lokuta suna far wa irin waɗanan mutane ne bayan sun yi bincike da fahimtar cewa za su samu kuɗin fansa mai gwaɓi.

Ya ce sarakunan da suke far wa masu daraja ta ɗaya ne da suke ganin suna da kuɗi mai yawa, kuma idan za a lura, “sarakunan na kauyuka ake ɗauka domin sun lura cewa ɗaukar ƙauyawa [talakawa] ba zai biya bukatunsu ba”.

“Sace irin waɗannan mutane na ƙara musu yawan kudin fasa da za su karba. Kuma a galibin lokuta da ɗan gari akan ci gari. Akwai haɗin bakin makusanta sarakuna wajen kai musu hari ko sace su”, in ji Dokta Muhammad.

‘Babu wanda ya tsira’

Masanin ya ce lura da yadda garkuwa da sarakuna ke sake girmama, “wannan na nuna cewa tsaro a Najeriya ya gama taɓarɓarewa domin a wannan yanayi da ake ciki babu wanda ya tsira”.

Ya nuna takaicinsa kan rashin isassun jami’an tsaro da kayan aikin zamani wanda yake cewa shi ke taka rawa a dimbin matsalolin da ake gani.

“Babu kayan aikin zamani, babu horo kamar yayda ake gani a ketare, ga rashawa, don haka matsalolin tsaro ba wanda nan kusa za a ga saukinsu ba ne.”

Amfani da kimiyya da fasaha

Dokta Muhammad ya ce masu bindigar nan sun wuce tunani domin ba wai kasafai suke kai hari ba, su ma suna amfani da hanyoyin zamani wajen ayyukansu.

Ya ce: “Baya ga makamai, alamomi na nuna cewa suna nazarin abubuwa da ke faruwa da amfani da jirage marasa matuka wajen satar bayanai kan abubuwa da ke faruwa kafin kai hari.

“Saboda haka sun fi karfin mahukunta da irin matakan da hukumomi ke dauka a yanzu, dole sai an tashi tsaye an haɗa-kai wajen yakar su.

“Sannan su kansu Fulani da ke daji dole sai sun taimaka wa hukumomi wajen yakar ‘ƴan binndigar da ke labewa a dazuka.”

Karin haske

Ana yi wa sarakuna kallo a matsayin masu taka muhimmiyar rawa wajen samar da masu aikin sa-kai da ke taimakawa wajen samar da tsaro, kamar bai wa mahukunta gudunmawa wajen dakile ayyukan ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fasa a fadin Najeriya.

Sai dai kamar yadda masana tsaro ke cewa far wa sarakunan a wannan lokaci babu shakka abin damuwa ne ga tsaron kasa ganin idan ba su tsira ba ina ga kuma mutanen da suke jagoranta.

Dama tuni mazauna kauyuka suke guduwa birane la’akari da rashin kwanciyar hankali, zaman zulumi da tunanin harin ‘ƴan bindiga.

Iyaye da dama sun cire yaransu daga makarantu a kauyuka saboda a kodayaushe sabon labarin garkuwa da dalibai bulla yake yi.

Sama da ɗalibai 1,000 aka sace domin neman kudin fansa daga Disamban bara zuwa wannan lokaci. Kusan 300 daga cikin wannan adadi da aka sace daga makarantu da ke jihohin Kaduna da Kebbi da Neja har yanzu na hannun ‘ƴan bindiga.

Gwamnati dai a kullum na cewa tana iya kokarinta wajen murkushe irin wadanan ɓata-gari ko ‘yan fasjhin daji kamar yadda ake kiran su. Sai dai korafe-korafe da zaman fargaba na karuwa.

Akwai masu cewa idan sarakuna ba su tsira daga irin waɗanan hare-hare ba da garkuwa da su ina ga mutanen gari – ko kuma talakawansu kamar yadda ake cewa a fada.

(BBC Hausa)

More from this stream

Recomended