Me zai faru a wasan Barcelona da Sociedad ranar Laraba?

Spanish La Liga

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Sociedad a gasar cin kofin La Liga da za su fafata a Camp Nou ranar Laraba.

Karawar ita ce ta mako na 19 da ya kamata su yi, amma za su buga wasan, bayan kammala gumurzun mako na 13 ranar Litinin.

Real Sociedad ce ke jan ragamar teburin La Liga da maki 26, bayan buga wasa 13 da nasara bakwai da canjars biyar aka doke ta wasa daya a kakar bana.

Barcelona tana mataki na takwas a teburi da maki 17, bayan buga wasa 11 da yin nasara biyar da canjaras biyu aka doke ta fafatawa hudu.

Atletico Madrid ce ta biyu da maki 26 iri daya da na Sociedad, sai dai kungiyar birnin Madrid tana da kwantan wasa biyu.

Sociedad ta ci kwallo 23 a raga a kakar bana, ita kuwa Atletico 21 ta ci, dalilin da ya sa kungiyar ta dare teburin La Liga.

Barcelona ta yi nasarar doke Levante da ci 1-0 a wasan mako na 13, ita kuwa Sociedad tashi ta yi 1-1 da Eibar ranar Lahadi.

Ranar Litinin aka raba jadawalin gasar Champions League karawar zagaye na biyu ta kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.

Kuma Barcelona za ta karbi bakuncin Paris Germain a wasan zagayen farko a Camp Nou da za su kara cikin watan Fabrairu, daga nan su buga wasa na biyu cikin watan Maris a Faransa.

Ita kuwa Sociedad tana buga Europa League za kuma ta fafata da Manchester United wadda ta bar buga Champions League.

Sociedad ta kwan da sanin kalubalen da ke gabanta a Camp Nou, kuma rabon da Barcelona ba ta yi nasara ba a irin wannan haduwar tun 1-1 da suka buga a La Liga ranar 27 ga watan Nuwamba 2016.

Sai da Barcelona na fuskantar kalubale a bana, inda kwanan nan Cadiz ta doke ta 1-0 a La Liga da rashin nasara da ta yi a hannun Juventus da ci 3-0 a Champions League a Camp Nou.

Sai dai kuma doke Levente da Barcelona ta yi a karshen mako ya kara mata kwarin gwiwar tunkarar Sociedad.

Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:

  • Iago Aspas Celta de Vigo7
  • Mikel Oyarzabal Real Sociedad7
  • Gerard Moreno Villarreal 6
  • Lionel Messi Barcelona5
  • Carlos Soler Valencia 5
  • Paco Alcacer Villarreal 5
  • Joao Felix Atletico Madrid 5
  • Luis Suarez Atletico Madrid 5
  • Cristian Portugues Real Sociedad 4
  • Manu Vallejo Valencia C.F 4
  • Jose Luis Morales Levante 4
  • Ansu Fati Barcelona 4
  • Marcos Llorente Atletico Madrid 4
  • Cristian Tello Real Betis 4
  • Karim Benzema Real Madrid 4
  • Angel Getafe CF4

More from this stream

Recomended