Kasuwar cinikin ‘yan ƙwallon ƙafa: Makomar Ozil, Rudiger, Ramsey, Camavinga, Umtiti, Hulk

Mesut Ozil

Kungiyar kwallon kafar DC United na cikin kungiyoyin da ke son daukar dan wasan Arsenal dan kasar Jamus Mesut Ozil, mai shekara 32. (DHA – in Turkish)

Juventus za ta iya sayar da dan wasan Wales Aaron Ramsey a bazara mai zuwa bayan dan wasan mai shekara 29 ya gaza tabuka komai tun da kungiyar ta saye shi daga Arsenal a 2019. (Mail)

Dan wasan Faransa Eduardo Camavinga ya shaida wa Rennes cewa yana son barin kungiyar a bazara mai zuwa. Kazalika Manchester United na son dan wasan mai shekara tmai shekara 18. (Mundo Deportivo via Sun)

Komawar Samuel Umtit Barcelona bayan jinyar da ya yi wata hanya ce ta barin kungiyar a watan Janairu, inda Everton da Juventus suke zawarcin dan wasan na Faransa mai shekara 27. (Sport – in Spanish)

Dan wasan Brazil Hulk, mai shekara 34, zai iya tafiya kungyar da ke gasar Firimiyar Ingila a watana Janairu bayan kwangilarsa ta shekara hudu ta kare a Shanghai SIPG ta China. (Sun)

Dan wasan Everton dan kasar Italiya Moise Kean, mai shekara 20, ya kama hanyar zaman dindindin a Paris St-Germain bayan tagomashin da ya samu tun da ya soma wasa a kungiyar ta Faransa wadda ta karbi aronsa. (Goal)

Leeds United na ci gaba da sanya ido kan Marcus Edwards, mai shekara 22, bayan dan wasan na Ingila ya bar Tottenham inda ya tafi kungiyar Portugal Vitoria Guimaraes a 2019. (Football Insider)

Kungiyoyin da ke buga gasar Firimiyar Ingila da dama na son daukar dan wasan Sifaniya Mikel Vesga, mai shekara 27, wanda kwangilarsa za ta kare a Athletic Bilbao a bazara mai zuwa. (AS – in Spanish)

More from this stream

Recomended