Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya bayyana cewa gobe Litinin za a soma horas da jami’an sabuwar rundunar SWAT da aka kafa wadda za ta maye gurbin SARS.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Frank Mba ya fitar, ya bayyana cewa jami’an da aka zaɓa waɗanda za su kasance cikin sabuwar rundunar matasa ne masu jini a jika kuma dukansu sun shafe aƙalla shekara bakwai suna aikin ɗan sanda.
Hakazalika ya bayyana cewa jami’an da aka zaɓa ba su da wani tabo ko kuma tarihi na laifi da suka aikata a baya, ba kuma a taɓa samunsu da laifin take haƙƙin bil adama ba ko kuma saɓa ƙa’idar amfani da makami.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an da aka zaɓa suna da cikakkiyar lafiya da za su jure namijin horon da za a ba su.
Za dai a soma horas da ‘yan sandan ne a kwalejojin horas da ‘yan sanda ta Ila Oragun, da ke jihar Osun da kuma kwalejin horas da ‘yan sanda ta jihar Nasarawa