Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, ya bayyana cewa man da aka samu a yankin arewacin kasar yana da yawa sosai.
A hirarsa da BBC, Shugaban kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana cewa za a amfana da yawan man da aka samu a arewa.
Tun a farkon watan Fabrairun bana, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin fara tonon rijiyoyin mai a yankin arewa maso gabas da ya hada da jihar Bauchi da Gombe da Yobe da Adamawa.
Kuma yayin da wasu ke zargin cewa siyasa ce kawai, Mele Kyari ya ce “ba a karya da fetir, kuma ba a boye shi, idan an same shi to an same shi.
Kuma ya ce man da aka samu a arewa yana da yawan da za a samu amfani daga gare shi. “Idan aka yi la’akari da yawan arzikin da aka samu, abin da aka kashe bai taka kara ya karya ba,” in ji shi.
Man fetur na daya daga cikin abubuwan da Najeriya ta dogara da shi domin samun kudaden shiga, kuma kasar na daya daga cikin mambobin kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur.