Bera ya jefa wani ango a halin ni-‘yasu

bera

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani mutum da ke daf da angwancewa ya shiga cikin halin ni ‘yasu bayan ya gano cewa bera ya cinye kudaden da ya dade yana tarawa.

Muhammad Asif wanda ya fito daga lardin arewa maso yammacin Khyber Pakhtunkhwa da ke Pakistan, ya tara kudade da suka kai dalar Amurka 3,000 inda ya ajiye su a cikin wani kwabet na katako a gidansa.

Kwanaki kadan kafin bikinsa, ya bude kwabet din domin dauko kudin, babban abin mamakin shi ne kawai sai yaga akasarin kudin bera ya cinyesu.

Kafofin watsa labarai a Pakistan sun shaida cewa Mista Asif ya dauki shekaru da dama yana aiki tukuru domin tattara wadannan kudade, yanzu sai ya kara wani aikin kafin tattara wadannan kudaden.

More from this stream

Recomended