Amurka: Dan bindiga ya hallaka mutum 5 a jihar Texas

Hakkin mallakar hoto
Reuters

‘Yan sanda sun ce wani harin bindiga da a aka kai a jihar Texas ta Amurka ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 5 da kuma raunata wasu da dama.

Wani mutum ne ya rinka harbin mai-uwa-da-wabi kan jama’a yayin da yake tuki a biranen Odessa da Midland, ranar Asabar.

‘Yan sanda sun ce an kashe wanda ake zargi da kai harin, sai dai ana ci gaba da bincike game da sauran wasu da ake zargi wadanda suka tsere.

Har yanzu ba a tabbatar da makasudin kai harin ba.

Mai magana da yawun ‘yansanda ya tabbatar da mutuwar mutum biyar da kuma raunata wasu guda 16. Ya kuma ce ‘yan sanda na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Wannan hari ya zo ne mako 4 bayan da wani dan bindiga ya kashe mutum 22 da raunata wasu guda 24 a garin El Paso na jihar Texas.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Shi dai maharin ya saci wata motar gidan waya ne, inda ya yi amfani da ita yana zagayawa tare da harbin mutane.

A wani sakon Tuwita, shugaban Amurka Donald Trump ya ce an sanar da shi game da harin.

More from this stream

Recomended