
Shugaban majalisar dattawa, sanata Ahmad Lawan ya ce ranar Laraba za a fara tantance sunayen mutanen da shugaban kasa, Muhammad Buhari ya aikewa majalisar a matsayin wadanda zai nada ministoci.
Lawan ya fadi haka ne bayan da ya gama karanto sunayen mutanen ya yin zaman majalisar na ranar Talata.
Shugaban majalisar dattawan yace majalisar zata dakatar da duk wani aikin dake gabanta domin gabatar da wannan muhimmin aikin da kasa take da bukata.
“Tantance mutanen da aka zaba a matsayin ministoci zai fara daga safiyar gobe,” ya ce.
Shugaban kasar ya tura sunayen mutane 43 da aka tsaba a matsayin wadanda za su zama ministoci, 12 daga cikin sunayen sun kasance ministoci a zangon mulkin Buhari na farko.