
Hakkin mallakar hoto
iStock / Getty Images
KLM ya ce ya dauki matakin ne domin fita hakkin fasinjoji
Kamfanin jirgin sama na KLM, ya yi kira ga mata masu shayarwa su rinka rufe jikinsu a lokacin da suke shayar da jariransu, sakamakon wani korafi da aka yi kan hakan.
Kamfanin KLM ya ce an amince da shayarwa a lokacin da mutane ke cikin jirgin, amma dole iyaye mata su rufe jikinsu matukar wadanda ke zaune kusa da su suka yi korafi ko bukaci su rufe jikin nasu.
Martanin kamfanin jirgin ya janyo zazzafar muhawara a shafin Twitter, inda wasu ke sukar wannan matakin.
Sai dai KLM ya shaida wa BBC cewa ya dauki matakin ne dan tabbatar da zaman lafiyar fasinjoji a lokacin da suke jirgin.
Mai magana da yawun KLM ta ce ”Ba dukkan fasinjoji ne suke sakewa ba a lokacin da ake shayar da jariri ko yara, kuma irin wadannan fasinjoji ne sukai korafi ga ma’aikatan jirgin. Don haka matakin an dauke shi ne dan ganin ba a takurawa kowa ba, tare da mutunta ra’ayin wadanda sukai korafin.”
Wannan mataki na KLM ya janyo ana tambayar kamfanin jiragen sama irin British Airways da EasyJet, kan na su tsarin na shayarwa a cikin jirgi.
Kamfanin British Airways ya shaida wa BBC ba zai taba daukar matakin hana iyaye mata shayar da jarirai a cikinsa ba, sai dai zai taimaka idan suka bukaci sirri a lokacin shayarwar.
Mai magana da yawun kamfanin ta shaida wa BBC cewa “A kowacce shekara jirginmu yana daukar dubban jarirai da yara kanana da iyalai kuma muna maraba da iyaye mata da ke shayarwa.”
A bangare guda kuma shi ma kamfanin jirgin sama na EasyJet ya ce daya daga cikin abin da jirginsu ya amince da shi shi ne maraba tare da taimakawa masu shayarwa, sannan dukkan fasinjoji suna da ‘yancin shayar da ‘ya’yansu nono a duk lokacin da suka bukaci hakan a cikin jirgin.
Ita ma ‘yar majalisa ta jam’iyyar Labour Stella Creasy ta wallafa a shafinta na twitter cewa matakin da kamfanin KLM ya dauka ya wuce makadi da rawa.