
Hakkin mallakar hoto
Reuters
A Libya ana kame ‘yan ci-rani sannan a tsare su a cibioyin da gwamnati ke kula da su
‘Yan Najeriya tara ne cikin akalla mutum 53 da aka kashe a harin da aka kai ta sama kan wata cibiyar tsare ‘yan ci-rani da ke Libya, wanda duniya ta yi Alla-wadai da shi.
Binciken farko-farko na jami’an diflomasiyyar Najeriya da suka ziyarci cibiyar a yankin Tajoura ya tabbatar cewa ‘yan kasar tara ne suka mutu a wannan hari, in ji ma’aikatar wajen Najeriya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce harin na daren Talata a Libya wanda a yanzu ya yi sanadin kashe akasari ‘yan ci-rani 53, na iya zama laifin yaki.
Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan kasashen duniya da kuma babban abokin gabarta Khalifa Haftar na zargin juna da kai harin.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata sanarwa daga ma’aikatar wajen Najeriya na cewa jami’an sun gano tare da karbo mata uku da wani namiji daya da wani dan karamin yaro da ke tatata, sai wani dan kimanin shekara 10.
Adadin mutanen da suka mutu a harin dai ya karu zuwa 53 daga adadin mutum 44, wasu fiye da 100 sun ji munanan raunuka.
Ma’aikatar wajen ta ce tana jiran jerin sunayen mutanen da ke cibiyar domin tabbatarwa ko akwai karin wasu ‘yan Najeriyar da harin ya ritsa da su.
Ta kuma bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa da nufin hukunta masu hannu a wannan aika-aika.
Kasar wadda rashin zaman lafiya ya tarwatsa bayan yamutsin da ya kai ga hambaras da Shugaba Mu’ammar Ghaddafi a shekara ta 2011, ta zama wata babbar hanyar da ‘yan ci-rani ke ratsawa.
Akasarin ‘yan ci-ranin na da burin isa kasashen Turai ne don samun rayuwa mai yalwa, amma sai su zama nama ga dumbin kungiyoyin sojin sa-kai da ke yunkurin kwace iko da arzikin man fetur na Libya.
Tarzoma ta karu ne bayan Janar Khalifa Haftar ya kaddamar da wani artabu don kwace Tripoli, babban birnin kasar inda gwamnatin da kasashen duniya ke marawa baya take da sansani.
Kungiyoyin kare hakin dan’adam sun ce ‘yan ci-ranin suna fuskantar mugun cin zarafi, kuma gararin da suke ciki ya karu bayan kaddamar da farmaki kan babban birnin.