Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai ce komai ba game da kunshin mutanen da za su kasance a sabuwar gwamnatinsa.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan da ya dawo daga kasar Birtaniya. Buhari ya ce a shirye yake ya zauna ya rantsar da sabbin ministocinsa.
Wani dan jarida ya tambaye shi “wadanne irin mutane ne za su kasance a cikin gwamnatinka da za a kafa?.” inda ya kada baki yace: “bazan fada maka ba.”
Kan yawan kashe-kashe dake faruwa a sassan kasarnan.Buhari ya ce ya lura Muhammad Adamu mai rikon mukamin babban sifetan ƴansanda na kasa ya rame wannan wata alama ce dake nuna cewa yana aiki.