Shugaban UBEC ya kubuta daga hannun masu garkuwa

Dr. Mahmood da Yasmin

An yi garkuwa da Dr. Mahmood ne tare da ‘yarsa Yasmin a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

BBC ta tabbatar da kubutar Dr Mohammed Mahmood Abubakar kwana daya bayan an yi garkuwa da shi tare da ‘yarsa Yasmin a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Dr. Mohammed Mahmood shi ne shugaban Hukumar Ilimin Bai-daya ta kasa wato UBEC.

An yi garkuwa da su ne yayin da suke koma wa gida Kaduna daga Abuja a ranar Litinin.

Wani da ya tasallake rijiya da baya ya shaida wa BBC cewa al’amarin ya faru da misalin karfe 3:00 na rana a kusa da garin Katari.

Ya ce ‘yan bindigar sun tare motoci kusan ashirin a duka hannu biyu a babban hanyar, kuma sun dauki mutane da yawa.

Yakubu Abubakar Sabo jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ya tabbatar wa da BBC kubutar shugaban UBEC din, inda ya ce mutum biyu ne aka jikkata.

A watan da ya gabata rundunar ‘yan sanda a Najeriya sun bayar da tabbacin cewa hanyar Kaduna zuwa Abuja ta yi lafiya.

Wannan ya biyo gomman mutane da aka yi garkuwa da su don neman kudin fansa, inda da dama suka rasa rayukansu.

A farkon watan Afrilu gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai ya ci karo da gungun masu garkuwar a kan hanyar, inda suka yi artabu da jami’an tsaronsa.

Mako daya kafin haka an sace mutum kusan 40 a lokaci guda a kan wannan hanya.

More from this stream

Recomended