Mutane biyar sun mutu a hatsarin mota a babbar hanyar Auchi-Okene

Mutane biyar ne suka mutu a wani hadarin mota da ya faru ranar Lahadi akan babbar hanyar Auchi zuwa Okene.

Kwamandan rundunar kiyaye afkuwar hadura ta tarayya,FRSC a jihar Edo, Anthony Oko wanda ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN faruwar lamarin a Auchi ya ce hatsarin ya faru da misalin karfe 11 na safe a mahadar Jattu dake karamar hukumar Etsako West dake jihar.

A cewar Oko mutane biyar sun mutu nan take a wurin ya yin da wasu shida suka samu raunuka daban-daban.

“Ina tabbatar maka da cewa mutane biyar ne suka mutu a wani hatsari da ya rutsa da ababen hawa da dama a yi mahadar Jattu dake kan babbar hanyar Auchi zuwa Okene.

“Wadanda suka mutu sun hada da mata uku da kuma maza biyu,” Oko ya ce.

Ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon shanyewar birkin wata motar daukar kaya mallakin kamfanin Dangote.

Kwamandan ya kara da cewa tuni aka gawarwakin dakin ajiye gawa.

More from this stream

Recomended