
Kasar Saudiyya ta bada hasken yiyuwar gina matatar mai, mai zaman kanta a Najeriya.
Khalid Al-falih ministan makamashi, masana’antu da kuma albarkatun kasa shine ya bada wannan haske ya yin wata ganawa da karamin ministan mai na Najeriya, Emmanuel Ibe Kachikwu a Riyadh babban birnin kasar.
A ranar Talatar da ta gabata ne Kachikwu ya gana da Al-falih da kuma wasu manyan shugabannin kamfanin Saudi Aramco wanda shine kamfanin mai da iskar gas mafi girma a duniya ta fannin samun kudin shiga ganawar ta mayar da hankali kan hadin kai tsakanin kasashen biyu ta fannin sarrafa mai da kuma iskar gas.
Kamfanin na kasar ta Saudiya yana fadada ayyukansa a fannin tace mai da kuma samar da sinadarai dake da alaka da man fetur kuma yana ganin Najeriya a matsayin wata kofa da zata bashi damar shiga sauran kasuwannin kasashen Afrika.
Da yake karin haske kan batun Kachikwu ya bayyana cewa Najeriya na kallon Saudiyya a matsayin kasa da ta samu nasarori a fannin mai da iskar gas.
Ya ce tuni Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai tabbatar da shirin kafa matatar ya tabbataa.