Kaduna: An sanya dokar hana fita a Kasuwan Magani

Gwamnan Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna a arewa masu yammacin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a garin Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kajuru.

Wani sako da gwamnatin ta wallafa a shafinta na twitter ya bayyana cewa dokar ta fara aiki ne nan take.

Sakon ya ce mataimakin gwamnan jihar Barnabas Yusuf Bala ya bada umarnin daukan tsauraran matakai wajen tabbatar da aiki da dokar.

Mataimakin gwamnan, wanda shi ne mukaddashin gwamnan jihar ya kuma yi kira ga jama’ar yankin su ba da hadin kai ga matakin domin maido da zaman lafiya a yankin.

Wasu bayanai da BBC ta samu daga wasu majiyoyin gwamnatin jihar sun tabbatar da cewa an dauki matakin ne domin hana bazuwar wani tashi hankali da aka fuskanta a yankin.

Wasu rahotannin kuma sun nuna cewa mutane sun jikkata a tashin hanakalin, to sai dai babu tabbas ko an samu asarar rai.

Me ke janyo tashin hankalin?

Yankin na Kasuwan Magani dake karamar hukumar Kajuru ya jima yana fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini.

Rikicin da yankin ke fama da shi dai ya ki ci – ya ki cinyewa ne sakamakon hare-haren ramuwar gayya da manyan kabilun da ke zaune a yankin ke kai wa juna.

Akwai dai zaman doya da manja da rashin yarda da ake yi tsakanin manyan kabilun yankin na Adara da Fulani.

Kowace kabila na zargin ‘yar uwarta da kai mata hare-hare, abinda ke haifar da ramuwar gayya.

Ko a farkon watan Aprilun nan, gwamnan jihar ta Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya roki jama’ar yankin da su daina kaiwa juna ramuwar gayya, saboda a cewarsa hakan ne ke rurua wutar rikicin.

Tashin hankalin da yankin ke fama da shi ya tilasta wa wasu mazauna kauracewa gidajensu, inda suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira.

Gwmanatin jihar tace tana yunkurin maganace matsalar tsaron, kuma tana aiki tukur domin kare rayuka da dukiyoyi ta yadda kowa zai zauna cikin gidansa lafiya.

More from this stream

Recomended