
An yi jana’izar mutum 19 da suka mutu sanadiyyar wani hadarin mota a karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa ranar Laraba.
Hadarin ya faru ne a garin Gwaram Sabuwa da misalin karfe 11:30 na dare, bayan da tayar gaban motar da ke dauke da fasinjoji 40 ta fashe.
Rahotanni sun ce daga nan ne sai motar ta wuntsula kafin ta kama da wuta. Mutum 21 daga cikin fasinjojin ne dai suka ji rauni.
Wani da abin ya faru a kan idonsa ya ce gawarwakin fasinjojin sun kone “kurumus ta yadda ba za a iya gane su ba.”
“Na ga gawarwakin jarirai shida tare da gawarwakin iyayensu,” in ji shi.
Mutanen da hadarin ya rutsa da su wadanda galibinsu mata ne da kananan yara suna kan hanyarsu ta dawowa daga daurin aure ne.