Kasar Brunei za ta fara aiwatar da shari’ar musulunci inda za a fara kashe ‘yan luwadi da
ma’aurata mazinata.
Sabuwar dokar waddda za ta fara aiki a ranar Laraba, ta hada da sauran laifuka wadanda suka
hada da yanke hannu.
Lamarin ya ja Allah wadai daga kasashen ketare. ‘Yan luwadin kasar sun bayyana damuwa da
sabuwar dokar. “Ka wayi gari kaga makwabtanka, ‘yan uwanka, da danginka suna tunanin cewa kai ba mutum bane kuma ya kamata a jefe ka”, a cewar wani dan luwadi dake zaune a kasar wanda ya nemi BBC ta sakaya sunansa.
Sarkin kasar, wadda take a kudu maso gabashin Asiya na nema a kara tabbatar da “koyarwa ta
addinin musulunci.” Ina fatan ganin koyarwar addinin muslunci ta karu a kasar nan a cewar Sarki Hassanal Bolkiah a cewar kamfani dillancin labarai ta AFP.
Luwadi laifi ne a kasar kuma ana hukunta masu laifin da hukuncin shekara 10 a gidan kaso. Musulmai ne kashi biyu cikin uku na mutanen kasar mai mutane 420,000.
Akwai hukuncin kisa a kasar amma ba a kashe kowa ba tun 1957.