Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai domin ganin an kawar da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC daga mulki a zaben 2027.
Tambuwal ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a lokacin da ya isa garin Sakkwato, inda dubban magoya bayansa daga jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara suka tarbe shi da waka da raye-raye, suna rike da tutoci da kuma kayan yakin neman zabe.
Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu da APC ba su da abin da za su iya bayarwa sai kara jefa kasar cikin wahala da talauci.
“Ina tunawa da irin gargadin da muka yi a 2023 cewa kada a zabi Bola Ahmed Tinubu saboda mulkinsa zai jefa kasar nan cikin abin da na kira Bola’s Garbage. Yanzu haka matsin tattalin arziki, yunwa da rashin fata da ake fama da shi a kasar nan shaida ce ta gaskiyar maganarmu,” in ji shi.
Ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su hada karfi da karfe wajen tabbatar da cewa APC da Tinubu sun sauka daga mulki a 2027.
“Manufarmu a bayyane take: dole mu hada kai mu kore APC da Tinubu daga mulki. Mu da abokan tafiyarmu za mu zagaya dukkanin sassan kasar nan domin ganin hakan ya tabbata. Ba za mu bari tsoron zalunci ya dakilemu ba, kuma ba za mu yi shiru mu bari wahalar ‘yan Najeriya ta ci gaba ba,” Tambuwal ya tabbatar.
Rahotanni sun ce tarbar da aka yi masa alama ce ta nuna karfin jam’iyya da magoya baya a arewa maso yamma yayin da ake kara shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaben 2027.
2027: Tambuwal Ya Bukaci ‘Yan Najeriya Su Hada Kai Domin Kawar Da Tinubu Da APC
