Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, tare da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, sun jagoranci taron shugabannin jam’iyyar daga jihar Kano domin tabbatar da gōyon bayansu ga sake neman takarar shugabancin ƙasa na Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Taron, wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, ya kuma mayar da hankali kan dabarun da za su taimaka wa jam’iyyar APC ta kwato mulkin Kano daga hannun jam’iyyar NNPP a zaɓen gwamnoni mai zuwa.
A cikin mahalarta akwai ministan kula da gidaje, Alhaji Abdullahi Atta; shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai, Abubakar Kabir Abubakar; tsohon gwamnan Kano, Kabiru Gaya; da kuma wasu ‘yan majalisu da tsoffin kwamishinoni.
Bayan kammala zaman, Ganduje ya bayyana cewa manufar taron ita ce haɗa kan shugabanni da kuma ƙarfafa kamfen don Tinubu.
Ya kara da cewa suna yaba wa manufofin gwamnatin Tinubu da ayyukan da ake gudanarwa a ƙasa da kuma a Kano. Ganduje ya kuma yi nuni da sauye-sauyen ‘yan siyasa daga NNPP zuwa APC a matsayin shaida cewa jam’iyyar na ƙara ƙarfi a jihar.
Haka kuma ya bukaci al’ummar Kano da su shiga rajistar masu kada kuri’a da ake gudanarwa yanzu domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu nasara a gaba.
A nasa jawabin, Barau Jibrin ya bayyana taron a matsayin wani mataki na dabarun siyasa don ƙarfafa tushen gōyon bayan Tinubu a Kano da Arewa baki ɗaya.
2027: Ganduje Da Barau Sun Jagoranci Taron Goyon Bayan Tinubu A Kano
