Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa ba shi da wata fargaba cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai kwace masa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2027 mai zuwa.
Obi ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kai kwalejin firamare ta LEA Primary School, da ke Kapwa, Abuja, inda ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa Atiku na shirin karbe tikitin takarar jam’iyyar. Ya bayyana Atiku a matsayin “babba ɗan uwa kuma shugaba mai daraja”.
Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan Atiku daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) suna komawa cikin gamayyar ADC domin shirye-shiryen zaben 2027.
Atiku ya taba bayyana a cikin hirarsa da BBC Hausa cewa ba zai ja da baya ba ga kowane dan takara, sai dai idan an doke shi a zaben fidda gwani na ADC — lamarin da ya tayar da cece-kuce a cikin ‘yan siyasa tare da haifar da sabuwar tattaunawa kan burinsa na 2027.
Da yake mayar da martani kan batun, Obi ya ce babu dalilin tsoro ko damuwa, domin burinsu na hada kai a karkashin ADC ba domin takara ba ne, sai domin ceto kasar Najeriya.
2027: Ba Na Tsoron Rasa Tikitin ADC Ga Atiku – Inji Peter Obi
