Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce ba ya cikin ’yan Arewa da ke haɗuwa domin cewa dole ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar mulki.
Sai dai Tambuwal ya bayyana cewa yana da cikakken ƙuduri, kashi 100 cikin 100, na ganin an sauya gwamnatin Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC ta hanyar dimokuraɗiyya a zaɓen shekarar 2027.
Da yake magana a wani shiri na gidan talabijin na Channels Television game da binciken da Hukumar EFCC ke yi masa, Tambuwal ya ce gwamnatin Tinubu ba ta jin daɗin ayyukansa a jam’iyyar adawa ta African Democratic Party (ADC).
Lokacin da aka tambaye shi ko binciken na EFCC yana da alaƙa da siyasa, Tambuwal ya amsa da cewa eh. Ya ƙara da cewa wasu mutane suna damuwa da irin rawar da yake takawa a siyasa, musamman saboda burinsa na ganin an canja gwamnati ta hanyar doka da tsarin dimokuraɗiyya.
Game da jita-jitar cewa wasu ’yan Arewa na haɗa kai domin kifar da gwamnatin Tinubu, Tambuwal ya ce gaskiya ne ’yan Najeriya ba su gamsu da halin da ake ciki ba, amma ya jaddada cewa shi yana cikin ƙungiyar ƙasa baki ɗaya da ke neman sauyin gwamnati ta hanyar kundin tsarin mulki a ranar 29 ga Mayu.
2027: Ba na cikin ’yan Arewa masu cewa dole sai Tinubu ya sauka ta kowane hali— Tambuwal

