Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai mara wa duk wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a 2026 baya, ko da kuwa shi ba ya daga cikin wadanda suka yi nasara ba.
Atiku, wanda yake daya daga cikin manyan jagororin hadakar jam’iyyun da ke karkashin ADC, ya bayyana haka ne a wurin taron maraba da sabbin wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar a jihar Legas ranar Asabar.
Taron ya samu halartar sakataren kasa na jam’iyyar, Rauf Aregbesola, da Sanata Kolawole Ogunwale, tare da shugaban ADC na jihar, Mista George Ashiru.
Atiku wanda aka wakilta da Farfesa Ola Olateju a wajen taron ya ce jam’iyya ce kadai za ta tantance wanda zai yi wa jam’iyyar takarar shugabancin kasa a 2027.
“It is not a thing we can predetermine. Whoever emerges through free and fair contests, we are all going to support,” in ji shi.
Ya ce dukkan masu neman takarar za su samu dama iri daya, domin babu wanda ake yi wa barazana ko ana kakaba shi kan jama’a.
“We are not imposing anyone on the people,” in ji Atiku.
Ya kara da cewa wanda ya lashe zaben fidda gwani zai zama wakilin dukkan ‘yan Najeriya a zaben 2027.
A cewar rahotanni, manyan ‘yan takarar da ake ganin za su fafata a zaben fidda gwanin sun hada da tsoffin gwamnoni da tsoffin ‘yan takarar shugaban kasa, Chibuike Amaechi, Peter Obi da kuma Atiku Abubakar kansa.
2027: Atiku Ya Ce Zai Mara Baya Wa Duk Wanda Ya Lashe Zaɓen Fitar Da Gwanin Shugabancin Kasa a ADC
