2027: APC Na Tilasta Wa ‘Yan Adawa Su Shiga Jam’iyyarsu – Dele Momodu

Masanin yada labarai kuma mai wallafa mujallar Ovation International, Dele Momodu, ya zargi jam’iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da tilasta wa ‘yan adawa shiga cikinta.

Momodu ya yi wannan zargi ne a ranar Juma’a yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Arise Television, inda ya bayyana cewa abin da ke faruwa yanzu tsakanin ‘yan siyasa ya zama abin mamaki.

Wannan furuci nasa na zuwa ne bayan wasu fitattun gwamnoni daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ciki har da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da takwaransa na Bayelsa, Douye Diri, suka sauya sheka zuwa APC.

Da yake mayar da martani kan yawaitar sauya shekar, Momodu ya ce, “APC tana jan kunne da kuma tilasta wa ‘yan adawa su shiga cikinta. Ina fara jin kamar an yi wa ‘yan Najeriya sihiri saboda dabi’ar da halayyar wasu ‘yan siyasa ba ta da kama da ta mutane masu hankali.”

Ya kara da cewa, “Mutanen da ba su da wani dalili na siyasa, ka yi tunanin gwamna mai wa’adi na biyu – ina yake gudu? Me yake guje wa? Wannan ya nuna abubuwa da dama ne suka hade. Wasu suna son jin dadi ne kawai, shi ya sa suke tafiya inda karfi yake. Kun san cewa gwamnatin tarayya tana da karfi fiye da shugaban kasar Amurka.”

A kwanakin baya, sauya shekar gwamnoni da dama daga jam’iyyun adawa zuwa APC ya tayar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke ganin hakan wani yunƙuri ne na jam’iyyar mai mulki domin karfafa matsayinta kafin zaben 2027.

More from this stream

Recomended