Ɗan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu.

Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar Zariya zuwa Kaduna.

A cikin wani sakon ta’aziya da ya fitar tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin amitattun na jam’iyar PDP, Adolphus Wabara ya bayyana rasuwar Faisal a matsayin wani babban rashi.

Hukumar FRSC dake kare afkuwar haɗura a titunan Najeriya ta bayyana cewa tayar motar da suke ciki ce ta fita abun da ya sa motar ta riƙa dungurawa.

More from this stream

Recomended