Ɗan majalisar tarayya daga Zamfara ya koma jam’iyar APC daga PDP

Sulaiman Abubakar mamba a majalisar wakilai ta tarayya ya sauya sheka daga jam’iyar PDP ya zuwa APC.

Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas shi ne ya sanar da sauya sheƙar a cikin wata wasika da ya karanta a zauren majalisar a zamanta na ranar Laraba.

Abubakar na wakiltar mazaɓar Gummi/Bukkuyum dake jihar Zamfara.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa rikicin cikin gida da  ya ƙi ci yaƙi cinyewa a jam’iyarsa ta PDP shi ne dalilin da yasa yanke hukuncin sauya sheƙar.

Ya ce yanzu haka jam’iyar PDP na da shugabanni biyu ne a mazaɓarsa.

“Ɗaya an cire shi ba tare da bin kundin tsarin mulkin jam’iya ba ɗayan kuma mun sauya sheka tare da shi.”a cewar wasikar da Abubakar ya rabutawa majalisar.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ya ƙalubalanci sauya sheƙar amma shugaban majalisar ya yi watsi da ƙalubalantar da ya yi.

More from this stream

Recomended