Ɗan gidan gwamnan Jigawa ya mutu a hatsarin mota kwana ɗaya bayan mutuwar kakarsa

Kwana guda bayan mutuwar mahaifiyarsa sai gashi gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya yi rashin ɗansa, Abdulwahab mai shekaru 24.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Hamisu Gumel ya fitar ya ce Abdulwahab ya rasa ransa ne a wani hatsarin mota a ranar Alhamis.

” A cikin alhini tare da miƙa kai ga ƙaddarar  Allah, Mai Girma, Mallam Umar Namadi gwamnan jihar Jigawa na sanar da sake mutuwar wani daga cikin iyalansa; ɗansa Abdulwahab Umar Namadi, ” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa marigayin ya rasu ne wani mummunan hatsarin mota da ya faru ranar Alhamis akan hanyar Dutse zuwa Kafin Hausa.

An yi jana’izar marigayin a garin Kafin Hausa.

More from this stream

Recomended