Sakamakon matsin lamba da jami’an tsaro suke yiwa ƴan fashin daji a jihar Kaduna hakan ya tilastawa gawurtaccen dan fashin daji,Lawal Kwalba da shi da mutanensa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro.
Wannan wata gagarumar nasara ce da aka samu yaƙin da jami’an tsaro suke da ƴan fashin daji a jihar ta Kaduna dama faɗin yankin da ayyukan ƴan fashin dajin ya yi ƙamari.
A yayin miƙa wuyar sojoji sun samu nasarar ƙwace bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, babur guda ɗaya gidan zuba harshi guda biyu daga hannun ɗan ta’addar da ya miƙa wuya.
Kwalba na tsare a hannun jami’an tsaro inda suke cigaba da ƙwaƙular bayanai daga wurinsa da za su taimaka wajen fatattakar saura ƴan ta’addar.