Amnesty International ta bayyana cewa ƴan sanda na Najeriya sun yi amfani da karfin iko fiye da kima wajen tunkarar masu zanga-zanga a lokacin zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar daga 1 zuwa 10 ga Agusta, inda aka kashe akalla mutane 24 a jihohin Borno, Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa, da Niger.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Isa Sanusi, ne ya bayyana wannan a lokacin taron manema labarai da gabatar da rahoton da aka sanya wa taken: “Agustar Jini: Mummunan Dakatarwar Gwamnatin Najeriya Kan Zanga-Zangar #EndBadGovernance,” wanda aka gudanar a Kano.
Rahoton ya kunshi bayanai game da mummunan tsaikon da aka yi wa zanga-zangar lumana da ake yi a kan cin hanci da rashawa da wahalar tattalin arziki.