Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara ta sanar da cewa jami’anta sun gano kan wani direban babur din haya, Rafiu Akano, wanda aka kashe a kauyen Asunlere, Oke-Oyi, a Karamar Hukumar Ilorin ta Gabas, Jihar Kwara, a ranar Lahadi.
Rafiu, mai shekaru 34, wanda kwanan nan ya sayi sabon babur don don neman kudi, ana zargin cewa wasu mutane uku sun kashe shi: Peter Samuel, Jeremiah Tiozinda, da Sunday Agbenke, wadanda aka kama su yanzu haka.
‘Yan sanda sun gano gawar gangar jikin marigayi mai babur din ba tare da kansa ba a wurin da lamarin ya faru ranar Litinin. Wadannan mutane uku da ake zargi sun amsa laifinsu, inda suka bayyana cewa sun jefa kan mamacin cikin kogi.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda, Ejire-Adeyemi Toun, ya fitar a ranar Asabar, rundunar ta ce, “Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara na sanar da al’umma wani ci gaba a binciken, inda masu bincike a SCID Ilorin suka gano sauran sassan jikin marigayi Rafiu Akano (M), mai shekaru 34, wanda aka kashe da mugunta ta hannun Peter Samuel (M), Jeremiah Tiozinda (M), da Sunday Agbenke (M) a ranar 4 ga Nuwamba, 2024.”