Ƴansanda sun kama mutane sama da mutane 30 saboda ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Gombe

Akalla mutane 31 ne rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama a yayin da take gudanar da samame kan maboyar masu safarar ƙwayoyi.

Da yake bayyana hakan a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mahid Abubakar, ya ce hedkwatar ‘yan sandan jihar Gombe ta hannun tawagarta ta ‘yan sintiri ta 999 sun kai samame kan wasu masu aikata laifuka inda aka kama su.

Ya bayyana cewa, samamen ya kai ga kamawa tare da dawo da wadanda ake zargi da shan miyagun kwayoyi.

A cewarsa, “A kokarin da ake yi na kare lafiyar jama’a da kuma yaki da miyagun ayyuka, da misalin karfe 10:00 na dare, tawagar, karkashin jagorancin jami’ai masu himma, ta kama mutane tara da ake zargin suna da hannu a ayyukan da suka shafi muggan kwayoyi.

“Daga cikin abubuwan da aka kwace akwai busassun ganyen da aka yi imanin cewa wiwi ne da kuma sauran abubuwa.”

More from this stream

Recomended