
Jami’an ƴansanda dauke da makamai sun dira gidan Sanata Dino Melaye dake Maitama a Abuja inda suka nemi kama shi.
Ƴansandan wadanda suka isa gidan a motoci biyar da misalin 12:30 kafin daga bisani su samu damar shiga gidan sanatan.
Jami’an tsaron sun yi amfani da motocin su biyu wajen toshe kofar shiga gidan sanatan inda wasu daga cikinsu suka tsaya a waje.
Daya daga cikin jami’an ƴansandan dake sanye da kayan gida wanda yaje wurin yan jarida ya ce sun je gidan ne domin kama sanatan da ya fito daga jihar Kogi.
“Mun zo nan ne domi kama Dino,”Dan sandan ya ce amma ya gaza yin bayani lokacin da yan jarida suka tambaye shi dalilin da yasa za su kama Dino.
Ƴansandan sun fadawa yan jarida musamman masu daukar hoto da su daina daukar su.