
Rundunar ƴansanda ta dakile wani shiri na wata zanga-zangar nuna goyon baya ga tsohon mai taimakawa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro,Kanal Sambo Dasuki mai ritaya.
Abdulsamad Dogondaji,shine wanda ya shirya zanga-zangar ya fadawa jaridar Daily Trust cewa an shirya gudanar da zanga-zangar ne ranar Talata, 23 ga watan Afirilu amma jami’an ƴansanda suka hana.
“Kwamishinan ƴansanda ya fada mana cewa har yanzu akwai zaman dar-dar bayan zagaye na biyu na zaben gwamna da aka gudanar a jihar kuma baza su bayar da dama ayi abin da zai kawo tabarbarewar doka da oda ba.
“Amma mun shirya yin zanga-zangar lumana ne shiyasa muka rubuta takardar neman izininsu da kuma samar da tsaro a lokacin zanga-zangar.”
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,DSP Muhammad Sadiq ya ce sun hana izinin ne saboda yanayi tsaro a jihar.