Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa an yi nasarar kawar da wani fitaccen dan bindiga a jihar Zamfara, Kachalla Sani Black.
‘Yan bangan da suka “gama” da dan ta’addan sun kuma kwato bindigogin AK-47 guda biyu, da tsabar kudi da ba a bayyana adadinsu ba da kuma bindigar PKT.
Ƴan banga na yankin sun kashe Kachalla da yaransa biyu a wani harin kwanton bauna da suka kai a Magama Mai Rake, a karamar hukumar Maru.
Kachalla Sani Black, babban dan gaban Bello Turji ne a harkar fashi, ya kuma kasance shugaban ‘yan fashi da ke aiki a Chabi, yankin Dan Sadau a karamar hukumar Maru.
Ƴanbanga sun sake kawar da wani ƙasurgumin ɗanbindiga
