Ƴan sandan Abuja sun ceto wani yaro ɗan shekara 4 da aka sato daga Ribas

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta ce jami’anta sun ceto wani yaro mai suna Hope Evans ɗan shekara 4 wanda aka bada rahoton bacewarsa a ranar 31 ga watan Oktoba daga makarantar firamare ta Azubie dake birnin Fatakwal a jihar Ribas.

A wani saƙo da aka wallafa a shafin X ranar Lahadi, Olatunji Disu kwamishinan ƴan sandan birnin ya ce ƴan sandan sun kuma kama wata mata mai suna Blessing Okoi mai shekaru 31 da aka zarginta da yin garkuwa da Evans.

Okoi ta ja hankalin yaron daga makarantar ta yin amfani da  biskit da ƙwai kafin ta gudo daga Fatakwal ta dawo Abuja.

Kwamishinan ya ce wacce ake zargin ta ɗauko Evans ne domin ta yaudari tsohon saurayinta ya yarda   cewa ta haifa masa ɗa.

An miƙa yaron ga mahaifiyarsa Lydia Jonah Gabriel.

More from this stream

Recomended