Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta ce ƴan ta’addan Lakurawa ne ke da alhakin kai harin bam da ya tashi akan titin Gusau-Dansadu a ƙaramar hukumar Maru ta jihar.
Muhammad Dalijan, Kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara shi ne ya bayyana haka hirar da aka yi ranar Alhamis a cikin shirin “Sunrise Daily” na gidan Talabijin na Channels.
Mutane 8 ne suka mutu a ranar Laraba bayan da wani bam ya tashi da su akan wata dake kan titin Gusau-Dansadu lokacin da suke tafiya a cikin wata mota ƙirar Golf.
Dalijan ya ce an hangi mayaƙan na Lakurawa a kusa da wurin da bam ɗin ya tashi ƴan sa’o’i kaɗan kafin fashewar inda ya ƙara da cewa ƴan fashin dajin da suke Zamfara basu da ƙwarewar ƙera bam.
Ya ce sakamakon fatattakar su da sojoji su ka a yi daga jihohin Sokoto da Kebbi shi ya sa waɗanda su ka rage a raye ke neman mafaka a dazukan Zamfara domin su sake tattaruwa.