Jami’an tsaro sun tsare kofar shiga fadar Sarkin Bichi gabanin isar sabon hakimin masarautar da aka naɗa.
Har ila yau jami’an ƴan sandan sun fatattaki dagatai da masu unguwanni daga cikin fadar waɗanda suka hallara a fadar domin tarbar sabon hakimin.
A wani ɓangaren shugaban ƙaramar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Maifata ya shawarci mutanen ƙaramar hukumar da su zauna lafiya kuma su ka sance masu bin doka da oda.
Shugaban ya sanar da ɗage ranar taron da aka shirya gudanarwa ranar Juma’a na tarbar sabon hakimin.
A wata sanarwa jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Tasiu Jibo Dawanau ya tabbatar da cewa yankin yana zaune lafiya a yayin da sauran al’umma ke cigaba da gudanar ayyukansu na yau da kullum.