
Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kashe wani mai suna Salisu Muhammad da aka fi sani da Dogo Saleh da ake zarginsa da zama gawurtaccen mai garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja.
A cikin wata sanarwa da ta fitar mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh ta ce an kashe wanda ake zargin a ranar 3 ga watan Maris lokacin da yake ƙoƙarin tserewa kamun da jami’an tsaro za su yi masa.
Jami’an ƴan sanda sun ce Dogo ne yake da alhakin garkuwa da mutane da dama a hanyar Abuja-Lokoja-Enugu da kuma wasu hanyoyin cikin birnin tarayya Abuja.
Adeh ta ce Dogo ya fito ne daga ƙauyen Babban Saural dake ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Rundunar ta gano bindigar AK-47 guda ɗaya da harsashi 61 da kuma kuɗi miliyan 3 a tare da shi.