Ƴan sanda sun kashe mutane biyu masu garkuwa da mutane a Imo

Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta ce jami’anta sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun  kuma ceto wasu mutane hudu bayan da aka yi musayar wuta.

A wata sanarwa ranar Asabar, mai magana da yawun rundunar, Henry Okoye ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne a Umuokanne, Ohaji dake ƙaramar hukumar Egbema ta jihar.

Sanarwar ta ce  jami’an sun kaddamar da farmakin da ya kai ga ceto mutanen bayan da suka samu kiran kai ɗaukin gaggawa ranar Asabar da ƙarfe 12:00 na rana dake cewa an yi garkuwa da wasu mata uku da namiji ɗaya Umuonkanne.

Har ila yau rundunar ta samu nasarar gano bindigar AK-47 guda ɗaya da harsashi guda 21.

An garzaya biyu daga cikin mutanen da aka ceto sun samu raunin harbin bindiga da suka samu a yayin da suke tsare a hannun masu garkuwar.

More from this stream

Recomended