
Ƴan sanda a jihar Borno sun kama wata mata mai suna, Falmata Muhammad mai shekaru 44 da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar caka masa wuƙa a garin Pulka dake ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 05:30 na ranar Alhamis.
“Wacce ake zargin ta farma mijinta Muhammad Malum mai shekaru 54 da wuka inda ta ji masa mummunan rauni a ƙirji,” a cewar rahoton ƴan sanda l.
Makama ya ce an garzaya da shi ya zuwa babban asibitin garin Gwoza inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Ya cigaba da cewa an ajiye gawar marigayin a asibiti domin gudanar da bincike dan gano musabbabin mutuwarsa.
Ya ƙara da cewa jami’an ƴan sanda daga ofishin ƴan sanda na Gwoza ne suka kamata biyo bayan ƙorafin da ƴan uwan marigyin suka yi kuka tuni aka gano sukar da aka yi kisan.