
Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta kama wata mata mai suna Fatima Muhammad mai shekaru 28 da ake zargi da shaƙe kishiyarta har sai da rai ya yi halinsa a unguwar Sarakuna dake cikin birnin Bauchi.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Ahmad Wakili a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce lamarin ya faru ne a gidan mijinsu a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Wakili ya ce a ranar 03 ga watan Maris ne mijin matar mai suna Saleh Isa ya miƙa ƙorafi gaban ƴan sanda inda yake nuna shakku kan musabbabin mutuwar matar tasa inda ya ce ƴan uwanta suna zargin kishiyarta na da hannu a mutuwar.
Bayan ƙorafin ne kwamshinan ƴan sandan ya tashi wata tawagar jami’an tsaro masu binciken laifi domin su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa Fatima Muhammad ce ta kashe Hajara.
Wakili ya ƙara da cewa a lokacin da take amsa tambayoyi Fatima ta amsa cewa ita ce ta shaƙe Hajara ta kashe ta kana daga bisani ta watsawa gawarta ruwan zafi tare da ƙona ta buhu.