Ƴan sanda sun kama wani mutum da aka ɗauka a bidiyo yana dukan wata matuƙiyar motar haya a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Friday Onu wanda aka ɗauki bidiyonsa yana dukan, Misis Yetunde Amole wata matuƙiyar motar haya a wani abu da hukumomin suka bayyana da cewa ya yi ƙoƙarin sace mata batirin mota ne.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kusa da Otal ɗin Oriental dake kan titin Lekki zuwa Epe.

A cewar ƴan sanda an kama Onu ne lokacin da yake ƙoƙarin cire batirin motar Amole abun ya jawo aka gwabza faɗa saboda ƙoƙarin da tayi na hana shi hoton fefan bidiyon faɗan ne ya karaɗe soshiyal midiya.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar mai magana da yawun rundunar Benjamin Hundeyin ya ce rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta yi allawadai da lamarin da kakkausar murya.

Ya ce jami’an ƴan sanda daga ofishin ƴan sanda na Maroko sun gaggauta zuwa wurin bayan samun rahoton faruwar lamarin kuma sun kama wanda ake zargin jim kaɗan bayan faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended