Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami’an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali  na Maiduguri.

Ɗaurarru da basu gaza 200 ne ba suka tsere daga gidan yarin biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye birnin a cikin watan Satumba.

A cikin wata sanarwa ranar Juma’a, Nahum Daso mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce Kur ya tsere ne bayan da kantangar gidan yarin ta rushe sanadiyar ambaliyar ruwan.

” Kur na zaman gidan yarin na Maiduguri kan laifin haɗa baki da kuma sata,” a cewar Daso.

Ya ƙara da cewa jami’an ƴan sanda dake sanya ido daga ofishin yan sanda na Gubio su ne suka samu ƙwararan bayanan sirri cewa  an ga Kur a garin Gubio abin da ya kai ga kama shi.

More from this stream

Recomended